Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta wallafa sunayen ‘yan takara na mukaman gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisun jihohin da za su shiga babban zaben kasar da za a yi a 2023.
Tun dai ranar Talata hukumar ta manna sunayen a ofisoshinta na jihohin kasar, amma a yammacin ranar Laraba ta wallafa dukkan sunayen a shafinta na intanet.
NABTEB Ta Saki Sakamakon Jarrabawar NBC/NTC Na 2022
Kwamishinan hukumar mai kula da yada labarai da ilmantar da masu zabe, Barista Festus Okoye ya sanar da haka cikin wata sanrwa da ya fitar:
“A takaice jam’iyyun siyasa 18 sun gabatar da ‘yan takara 837 da kuma mataiamakansu a zabukan gwamnoni 28 da za a ayi a watan Fabrairun 2023. Ga zabukan ‘yan majalisar jihohi, ‘yan takara 10,231 ne ke shirin fafatawa kan kujeru 993.
Ya kuma ce jerin sunayen, wanda ya kai yawan shafi 894, an wallafa shi a shafin hukumar.
