Connect with us

News

ASUU za ta kai karar gwamnati kan rijistar sabbin kungiyoyin malaman jami’o’i biyu .

Published

on

DAGA   KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU za ta kai karar gwamnatin kasar kan rijistar da ta yi wa sabbin kungiyoyi na malaman wato CONUA da NAMDA ( Congress of Nigerian Universities Academics, da National Association of Medical and Dental Academics)

Lauyan kungiyar ta ASUU, Femi Falana, shi ne ya bayyana haka a wata hira ta tashar talabijin ta Channels Television, a yau Alhamis, inda ya ce za su kalubalanci yi wa kungiyoyin biyu rijistar.

Advertisement

Dan Wasan Chess Da Ake Zargi Da Magudi Ya Yi Biris Da Martanin Mutane

A ranar Talata ne ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayar da takardar shedar rijista ga sabbin kungiyoyin biyu da ke zaman kamar kishiyoyi ga ASUU.

A lokacin da yake ba su takardar Ngige, ya ce kungiyoyin biyu za su wanzu kafada da kafada da ASUU>

Ita dai ASUU tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, inda mambobinta wato malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da aiki a kan kin biyansu kudaden alawus-alawus tare da neman kyautata jin dadinsu da sauran bukatu daga gwamnatin tarayya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending