Business
Zaman lafiya ya dawo a masana’antar siminti ta Dangote a Obajana
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Zaman lafiya na dawo wa a kamfanin yin siminti na Dangote a Obajana, bayan yunkurin rufe kamfanin da wasu matasa suka yi a ranar Laraba.
A ranar Larabar ne dai wasu matasa a jihar Kogi, tare da wasu gungun ƴan vigilante su ka mamaye harabar kamfanin a kokarin rufe shi.
Ƙananan yara miliyan goma na fama da yunwa a Gabashin Afirka – rahoto
Majalisa Dokokin jihar ce ta bayar da umarnin rufe kamfanin Dangote a ranar Talata, bayan da ta ba da umarnin rufe shi bisa zargin badaƙala wajen mallakar kamfanin da ga rukunin kamfanunuwa na Dangote.
Sai dai kuma a yau Juma’ar da ne al’amura su ka fara dawo wa daidai a kamfanin, tare da tsare kofofin da jami’an tsaro dauke da makamai.
Wata majiya ta kusa da kamfanin ta bayyana wa NAN cewa kamfanin na kokarin ci gaba da gudanar da harkokinsa na yau da kullum bayan tarzomar da a ka samu a ranar Laraba.
“Kamar yadda ku ke gani, kwanciyar hankali ya dawo a kamfanin simintin Dangote a nan Obajana.
“Damuwarmu ita ce fiye da mutane 26 na kamfanin da aka harba a harin, ba su ji ba ba su gani ba a ranar Talata.
“Ba wai kambama wa mu ka yi ba saboda mu na da dukkan hotunan wadanda suka jikkata. An garzaya da wasu daga cikin wadanda aka harben zuwa asibitin kwararru dake Lokoja,” inji shi
