Connect with us

News

2023: Za Mu Hana Baki Yin Zabe A Najeriya —Imigireshan

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, ta kuduri aniyar hana wadanda ba ‘yan Nijeriya ba kada kuri’a a zaben shekara ta 2023, tare da alkawarin tabbatar da ganin an yi zabubbuka cikin gaskiya da sahihanci.

Mataimakin Kwanturola-Janar mai kula da shiyya ta uku ACG Isma’ila Abba Aliyu ya sanar da haka a Damaturu na Jihar Yobe, inda ya ce Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hana wadanda ba ‘yan Nijeriya shiga zabe ba.

Ba mu da shirin tayar da hatsaniya a zaben 2023 – IPOB

Ya ce ko a lokacin yakin neman zabe, jami’an su za su sa ido domin tabbatar da ganin baki ba su shiga cikin harkokin siyasa ba, saboda wannan ya na daya daga cikin lokuta masu mahimmanci.

Isma’ila Abba Aliyu, ya ce za su kuma yi amfani da na’urorin zamani domin sa ido a kan motsin mutanen da ake shakku a kan su, kuma dole ne su yi bayanin kowa domin kauce wa yin barna da sunan Nijeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending