News
2023: INEC ta kashe duk wata hanyar da za a iya yin maguɗin zaɓe -Farfesa Yakubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bugi ƙirjin cewa INEC ta samu nasarar toshe duk wata ƙofar da za a iya yin maguɗi a zaɓen 2023.
Da ya ke jawabi a wani taron da aka shirya a Cocin St. James na Ɗariƙar Angalika da ke Asokoro, Abuja a ranar Lahadi, Yakubu ya ce INEC ta samu wannan gagarimar nasara ce ta hanyar ƙirƙiro tsarin tantance mai rajistar zaɓe na ƙeƙe-ƙeƙe, wato BVAS.
Ana zaman dar-dar a Mozambique bayan bacewar zaki
Yakubu wanda Mataimakin Kakakin Yaɗa Labarai na INEC da kuma Wayar da Kai, Chukwuemeka Ugboaja ya wakilta, ya bugi ƙirjin cewa tsarin tantance mai karin rajistar hikima ce da basirar injiniyoin INEC ta kai su ga kirƙiro shi.
Daga nan ya ce BVAS zai ƙara wa INEC ƙarfin guiwar tabbatar da cewa ta shirya zaɓe sahihi, wanda babu yadda za a iya yin maguɗi lokacin zaɓe.
“Abu na biyu da zai ƙara wa zaɓen 2023 inganci shi ne sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022. Sashe na 9 (6) ya bai wa INEC ikon daina yi wa mutane rajista kwanaki 90 kafin zaɓe. Daga nan ne kuma sai hukumar ta tankaɗe tare da tace rajistar ɗungurugum.
“Kuma mutane su fahimci cewa INEC ba ta iya soke rajistar kowa. Amma ta na da ikon soke rajistar wanda ya yi rajista sau biyu.
“Hanya ta uku da za a kawo ƙarshen maguɗin zaɓe, ita ce aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na’urorin kafafen sadarwa na zamani daga rumfar zaɓe.
“Sannan kuma Sashe na 51 na Dokar Zaɓe ta 2021, ya nuna ƙin amincewa da sakamakon zaɓen inda adadin ƙuri’un da aka jefa a akwati su ka haura adadin yawan waɗanda aka tantance ta tsarin BVAS.
“Sannan kuma a zaɓen 2023, Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2023 ta haramta wa INEC karɓar sakamakon da aka tilasta wa jami’in zaɓe bayyana sakamkon zaɓe.”
Ya buga misali da zaɓen sanata na Jihar Imo a 2019, wanda duk da cewa tilasta jami’in INEC aka yi ya karanta sakamakon zaɓe, amma kotu ta amince da sakamakon. Ya ce a yanzu ƙarƙashin sabuwar dokar zaɓe, hakan ba zai yiwu ba.
Daga karshe ya yi kira ga manya da masu ilmi mazauna cikin birane cewa su daure, su riƙa fita su na jefa ƙuri’a a ranar zaɓe.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
