Connect with us

News

Ba za mu cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa ba – Gwamnatin Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasar.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato wata sanarwa da hukumar ta fitar, in da bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa za ta yi hakan.

Advertisement

Ƴan sanda sun cafke ɗan shekara 18 bisa zargin kashe abokinsa a Kano

Wannan dai martani ne ga rahotannin kafafen yada labarai da ke bayyana cewa gwamnati na shirin cefanar da kamfanin, inda rahotannin suka ce za a yi hakan cikin watanni masu zuwa.

Advertisement

”Gwamnatin tarayya ba ta da shirin sayarwa ko kuma cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa, kuma babu wani daga gwamnatin da ya sanar da hakan,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaba Buhari na mayar da hankali kan zamanantar da bagaren wutan lantarki na kasar ta hanyar bijiro da tsare-tsare wanda ya hada da hadin gwiwa da shirin inganta wuta na ofishin shugaban kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending