Wata babbar kotun tarayya da ke zama a garin Dutse ta wanke tsohon gwamnan jihar Jigawa Saminu Turaki daga tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta almundahana da kuɗi naira biliyan 8.3.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ce ta kai tsohon gwamnan, da wasu kamfanoni uku, ƙara tun a shekara ta 2007 kan laifuka 33.
An Yi Garkurwa Da Hafsan Dan Sanda A Kwara
Alƙalin da ya yanke hukunci, mai shari’a Hassan Dikko, ya yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da ake wa tsohon gwamnan bisa hujjar rashin mayar da hankali daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara.
Bugu da ƙari kotun ta umurci a mayar wa Saminu Turaki takardunsa na tafiye-tafiye
