News
NNPC ya fara shirin gyaran matatar man fetur ta Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin Nijeriya ta amince da ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta jihar Kaduna.
Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi.
A ƙarshen shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta ware fiye da dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai ta da ke birnin Fatakwal, aikin da ta ce ana ci gaba da yi.
Kazalika, za a ci gaba da irin wannan aiki a matatar ta garin Warri na Jihar Delta
-
News7 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News6 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News7 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

