Connect with us

News

Kotu a Bauchi ta yanke wa wani saurayi da ya kashe abokinsa hukuncin kisa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Advertisement

 

Wata babbar kotu a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kama shi da laifinsa kashe abokinsa.

Advertisement

Jaridar Punch ta ruwaito a yau cewa alkalin da ya yanke hukuncin Mai Shari’a Faruq Sarki, ya samu mutumin da laifin kashe abokin nasa ne ta hanyar yanka wuyansa da ƙwaƙule masa ido ya saka su a cikin kwalba kafin daga bisani ya binne shi a wani wajen daban.

Kwankwaso ya ƙaddamar da manufofinsa na takarar shugaban Najeriya

Advertisement

Lauyoyin da suka shigar da ƙarar daga Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi, Mohammed Ibrahim da Salihu Haruna da Ali Yusuf sun zargi saurayin da kisan kai inda suka kafa hujja da cewa shi ma hukuncinsa kisa ne idan aka yi la’akari da sashe 221 na kundin dokar Penal Code.

Masu shigar da ƙarar sun shaida wa kotu cewa wanda ake zargin mai suna Musa Hamza ɗan ƙaramar hukumar Alkaleri, ya yaudari abokin nasa Adamu Ibarhim mai shekara 17, ya dake shi a ido da wani sanda sannan ya cire kansa da idanuwansa biyu, daga bisani kuma ya binne shi.

Advertisement

Da farko dai matashin ya yi watsi da zargin da ake yi masa ɗin a gaban kotun, amma daga baya ya amsa laifin.

Masu shigar da ƙarar sun gabatar da shaidu shida a yayin shari’ar yayin da mai kare wanda ake ƙarar ya gabatar da shaida ɗaya kawai.

Advertisement

Shaidun sun ce mahaifin yaron da aka kashe ɗin ya kai ƙorafin cewa ɗansa bai koma gida ba, amma ya samu bayani cewa an gan shi da wan ake zargin a tare da daddare.

Daga baya an tsannanta bincike inda aka gano wayar marigayin a hannun wanda ake zargi da kashe shin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending