News
Mutane 14 Sun Kone Kurmus A Hadarin Mota A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Fasinjoji 14 ne suka kone kurmus a hanyar Gaya zuwa Wudil a wani hatsarin mota kirar Toyota Hummer da wata mota kirar Hyundai jeep. FRSC ta tabbatar wa SOLACEBASE.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa motar bas mai lamba GML 102 TA mallakin Kano Line ta taho ne daga jihar Gombe a yayin da ta yi karo da wata motar kirar jeep, da misalin karfe 7:30 na daren Lahadi.
Yan wasan gaba tara zamuje dasu Qatar cewar kocin Brazil
Kwamandan hukumar FRSC reshen Kano, Zubairu Mato ya shaida wa SOLACEBASE ranar Talata cewa jami’an kiyaye haddura sun isa wurin da hadarin ya afku a kauyen Rege da ke Antukuwani, kan hanyar Kano zuwa Gaya da karfe 7:45 na yamma.
“Fasinjoji 13 ne suka kone kurmus nan take tare da jikkata wasu 6 a hadarin,” inji Mato.
An sanar da SOLACEBASE rasuwar daya daga cikin fasinjojin, macen da ta rasu a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH) a sashin ICU
Kwamandan FRSC ya alakanta hadarin da wuce gona da iri
Ya kuma bukaci direbobi da su tabbatar da amfani da na’urar da za ta iya kayyade saurin gudu a kodayaushe tare da kaucewa hadari
