Connect with us

News

Mun saka Ido Sosai kan labaran karya da kamfanin Twitter ke fitar wa

Published

on

Ministan yada labarai Lio Muhammad

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin tarayyar Nigeria tace tana saka Ido kan katafaren kamfanin Twitter kan labaran kanzan kuregen dake fitar wa bayan sauyin siyan da hamshagin dan kasuwarnan  Elon musk yayi 

Advertisement

 

 

Advertisement

A jiya  Alhamis ne Ministan yada labarai,da raya Al,adu na nigeria Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana matsayin gwamnatin su a kan wannan batu a wani taron manema lanbarai a Abuja.

Muryar amurka ta rawai to cewa Ministan ya ce rufe dandalin sadarwar a bara ga masu amfani da shi ya biyo bayan yunkurin da wasu bata gari suke yi na haddasa tashin hankali a Najeriya da labaran kanzon kurege da yada bayanan karya da na kiyayayya

Advertisement

Hatsarin mota ya ƙona mutum 11 ƙurmus a Jihar Kogi

 

Advertisement

 

Lio ya yi gargadi cewa gwamnati bata da niyar hana duk wata kafar sadarwa gudanar da ayyukanta, amma kuma hakan ba zai sa ta kyale a yi amfani da wani dandalin sadarwa a jefa kasar cikin rikici da bala’i ba

Advertisement

 

Ministan ya ce: “Mutane da dama sun yi waya suna tambayarmu ko me zai kasance yarjejeniyar mu da Twitter saboda sauyin mallakarsa.”

Advertisement

 

“Wasu da dama kuma sun nemi jin martanin mu bayan rahotannin da ke nuna cewa an samu karuwar labaran kanzon kurege, da yada bayanan karya da kuma kalaman nuna kiyayya tun lokacin da shahararren dandalin sadarwa ya sauya ikon mallakarsa.”

Advertisement

 

Ya kara da cewa, “wasu mutane da yawa ma sun tambaye mu ko zamu sake hana Twitter aiki?.

Advertisement

 

Ya bayyana cewa, gwamnati tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter, kuma ko kadan, ba nufinta bane ta haramta duk wani dandalin sada zumunta ba ko kuma murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki.

Advertisement

 

A cewar Muhammed duk  abin dake faruwa yanzu a shafin Twitter sananne ne ga kowa. Twitter ya zama dandalin zabi ga masu son tada zaune tsaye a Najeriya, ta hanyar yin amfani da labaran karya, da kalaman kiyayya.

Advertisement

 

Ya kara da cewa, babu wata al’umma da za ta kyale wani dandalin sada zumunta ya jefa ta cikin rudani. Tabbas ba Najeria ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending