News
Yau Ake Fara Hako Danyen Mai A Arewacin Najeriya
A yau ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin hakar danyen mai na farko a yankin Arewacin Najeriya.
Fara hakar danyen man a Rijiyar Mai ta Kolmani 809 da 810 da ke jihohin Bauchi da Gombe na zuwa ne kimanin shekaru shida bayan gano wasu rijiyoyin mai a Arewacin Najeriya a 2016.
KASHI 60 BISA DARI NA YAN AREWA BASU DA ASUSUN AJIYA A BANKI~ Sanata Uba Sani
Kimanin shekara biyu ke nan da dakatar da makamancinsa da aka fara a Jihar Borno, sakamakon matsalar rashin tsaro.
Kamfanin mai na NNPC ya gano arzikin mai da yawansa ya kai na kasuwanci a Arewacin Najeriya ne a jihohin Neja a yakin Arewa ta Tsakiya sai kuma Borno, Bauchi da kuma Gombe a yankin Arewa maso Gabas.kamar yanda yaridar Aminiya ta rawaito
Arzikin man Najeriya
Tun daga lokacin da aka fara hako danyen mai a Najeriya ya zama babbar hanyar samun kudaden shigar da gwamnatin kasar ta dogara da ita.
Kamfanin NNPC ya yi hasashen arzikin man da ke karkashin kasa a Najeriya ya haura lita biliyan 50.
Tuni dai kasar Jamhuriyyar Nijar, makwabciyar Najeriya ta yakin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, ta gano mai a yankin ta kuma fara hako shi.
Hakan ya kara wa Najeriya kwarin gwiwa a hasashenta na samun mai a yankin.
Alfanon arzikin mai
Danyen mai shi ne makamashin da aka fi amfani da shi a duniya, don haka yake zaman babbar hanyar kudaden shigar kasashe.
A Najeriya, gwamnati tarayya kan ware wa jihohi masu arzikin mai kashi 13 cikin 100 na kudaden da aka samu daga bangaren mai.
Illar arzikin mai
Sai dai kuma yankunan da ake hakar man sukan yi fama da matsalolin gurbacewar muhalli sakamakon ayyukan hakar man.
A kan haka ne aka yi ta samun yawaitar korafe-korafe a yankin Neja Delta da aka fara samun mai.
Zargin kamfanonin hakar mai da lalata musu muhalli ba tare da biyan su wata diyya ba ya haifar da matsalar tsaro inda wasu bata-gari kan fasa bututun danyen mai domin su sace.
Akwai kuma matsalar masu satar man da ake zargin suna hadin gwiwa da jami’an tsaro.
Shin an dauki darasi
Haka ne ma ya sa ake ganin ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan da suka dace a yankin Arewa maso Gabas da aka gano rijiyoyin danyen mai domin hana aukuwar irin matsalar da aka samu a yankuna masu arzikin mai a yankin Kudu.
makomar danyen mai
A halin yanzu kasashen Turai na kokarin ganin an daina amfani da shi zuwa wasu shekaru a nan gaba, a koma amfani da makamashin tsirrai da kuma hasken rana.
Ana yin wannan gangami ne da zummar takaita sauyin yanayi da ake dangantawa da hayakin da injina ke fitarwa.
Hakan na nufin nan gaba farin jini da kasuwar danyen man za su ragu a kasuwar duniya, wanda kuma zai kawo nakasu ga kudaden shigar gwamnatocin da suka dogara da shi
