News
Gobara ta kashe mutum 10 sakamakon dokar kullen korona
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda sabuwar zanga-zangar adawa da kullen korona ta ɓarke a birnin Urumqi na ƙasar China.
Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da wata gobara da ta tashi a wani gini ranar Alhamsi ta kashe mutum 10 a birnin.
Za’a cigaba da fuskantar wahalar man fetur har zuwa sabuwar shekara.
An ga masu zanga-zangar na fuskantar jami’an tsaro, yayin da suke karya shingayen da aka kafa tare da ihun ”a kawo ƙarshen kullen korona”.
To sai dai hukumomin birnin na Urumqi sun musanta zargin cewa dokar kullen ce ta hana mutanen kuɓucewa gobarar.
Birnin wanda ke yammacin ƙasar na cikin dokar kullen korona tun farkon watan Agusta.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
