Connect with us

Sports

Hankalin Ronaldo ya rabu, Man Utd na tattaunawa kan Gakpo

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

Cristiano Ronaldo, ya samu tayi daga kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya wadda za ta ba shi kudin da ya kai fam miliyan 150 a shekara, bayan rabuwarsa da Manchester United.

 

Advertisement

Dan wasan na Portugal na dab da cimma yarjejeniya da kungiyar ta Saudi Arabia.

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano sun ci zarafin Shugaban Hukumar da aka dakatar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado.

Sai dai kuma ana ganin tauraron na Portugal har yanzu yana son taka leda a gasar Zakarun Turai saboda haka har yanzu bai yanke shawara kan ansar wannan tayi ba.

 

Manchester United na tattaunawa da wakilan dan gaban PSV Eindhoven Cody Gakpo kan sayen dan wasan na Netherlands a watan Janairu.

 

Watakila matashin dan wasan tsakiya na Brighton Billy Gilmour dan Scotland ya tafi Villarreal aro a watan JanairuDan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets, na sha’awar tafiya kungiyar Inter Miami ta gasar Amurka idan kwantiraginsa ya kare da Barcelona a watan Yuni.

Advertisement

 

 

 

Dan gaban kungiyar Los Angeles FC Gareth Bale, zai yanke shawara game da kungiyarsa a watan Fabrairu bayan da ya gaya wa Wales cewa yana sha’awar ci gaba da taka wa yankin leda.

 

Liverpool za ta dauki tsohon mai yi wa Arsenal zawarcin ‘yan wasa Sven Mislintat, wanda ya yi aiki da Jurgen Klopp a Borussia Dortmund, a matsayin wanda zai maye gurbin Julian Ward darektan wasanninta.

Advertisement

 

Wakilin dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie, wanda ya bar AC Milan zuwa Barcelona a watan Yuli ya kawar da yuwuwar komawar dan wasan Italiya sakamakon rahotannin da ke cewa Inter Milan na zawarcinsa.

 

Manchester United ta bi sahun Arsenal a zawarcin matashin dan bayan Scotland Jack Wylie mai shekara 15 daga Rangers.

 

Darektan wasanni na Barcelona Jordi Cruyff ya ce taurarin na Sifaniya na bin diddigin matashin dan wasan tsakiya na Ghana Mohammed Kudus dan Ajax.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending