News
A’isha Buhari: Dole ne a saki Aminu – Amnesty
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su saki matashin nan da ake zargi da cin mutuncin uwargidar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari tare da yin watsi da duk zarge-zargen da ake yi masa.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an azabtar da matashin bayan kama shi.
Ta ce “babban abin kunya ne a ce hukumomin Najeriya sun kama tare da azabtar da Aminu Adamu kawai saboda ya wallafa bayanai a shafin tuwita wanda ya shafi uwargidar shugaban ƙasar.”
Bayanin ya ƙara da cewa wannan lamari karan-tsaye ne ga ƴancin bil’adama.
Haka nan hukumar ta ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su mayar da hankali a kai shi ne tsarewar da aka yi wa matashin ba bisa ƙa’ida ba da kuma azabtar da shi da aka yi.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa kotu ta tura matashin mai suna Aminu gidan gyara hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin sa da cin mutuncin mai-ɗakin shugaban ƙasa, A’isha Buhari a shafinsa na tuwita.
