News
Wani dan majalisar dokokin Senegal ya doki takwararsa a zauren majalisa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An samu yamutsi a zauren majalisar dokokin Senegal ranar Alhamis bayan wani dan majalisa ya doki takwararsa a ka a yayin da ake nuna zaman majalisar kai-tsaye a talabijin.
An fuskanci tsaiko a zaman majalisar lokacin da ake gabatar da kasafin kudi, bayan dan majalisar dokoki daga jam’iyyar hamayya Massata Samb ya bar dandamali inda ya tafi wurin ‘yar majalisa Amy Ndiaye Gniby ta jam’iyyar Benno Bokk Yakaar mai mulki sannan ya doke ta a ka.
Da take mayar da martani, Ms Gniby ta jefi Mr Samb da kujera, kafin wasu ‘yan majalisar su sanya baki, amma rikicin bai tsaya ba domin kuwa sun yi ta nuashin juna, lamarin da ya sa aka soke zaman majalisar.
Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito cewa Mr Samb ya tuna wa zauren majalisar wasu kamalai da Ms Gniby ta yi tun da farko wadanda ya ce na “rashin da’a ne”.
Daga nan ne Ms Gniby ta mayar da martani daga kujerarta inda ta ce ba ta “damu” ba.
Nan take Mr Samb ya daina magana ya ruga a guje inda take.
