Connect with us

News

Ina fargabar sakamakon zaɓen 2023 – Jega

Published

on

Jega

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya nuna fargaba kan sakamakon zaben 2023 sabo da abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa a Nijeriya.

Mutum Miliyan 25 Ke Dauke Da Cutar AIDS A Afirka —WHO

A cewar Jega, yana matukar fargabar yadda sakamakon zaben  zai kasance.

 

Advertisement

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron lakcoci da Electoral Hub ta shirya a Abuja a jiya Laraba.

 

A cewar Jega, duba da yadda ake faɗan siyasa a jihohi da kuma kona ofisoshin INEC, shi ne abin ya ke bashi tsoro.

 

Sai dai Jega ya nuna kwarin gwiwa cewa Nigeria za ta yi zabe lafiya da kuma samun zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

 

Advertisement

“Ina da matukar fargaba game da sakamakon zaben. Amma za ku ga mutane irina su ne waɗanda zan kira masu kyakkyawan fata game da makomar kasarmu.

 

“Don haka ina fatan duk da sakaci da muke gani, barnar da muke ganin da yawa daga cikin wadanda ake ce wa manyan ‘yan siyasarmu suke yi, muna fatan jama’a za su tashi tsaye su tsunduma cikin harkar zabe yadda ya kamata, ta yadda za mu yi zabe. Ku samu sakamako mai kyau a 2023, “in ji Jega.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending