Connect with us

News

Obasanjo Ya Ce Tasirin Najeriya Na Raguwa A Idon Duniya   

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Masana harkokin difplomasiyya a kasar nan, sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan wani furuci da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi cewa tasirin Najeriya a duniya yana raguwa, musamman ma a kan kasashen nahiyar Afirka.

Advertisement

 

Wasu masana na ganin cewa akwai gaskiya a cikin maganar, suna danganta lamarin da rashin ƙwararrun masu ba da shawara ga shugabanni da kuma rashin aiki da ita idan an ba su.

Advertisement

Yawan matan da ke mutuwa yayin haihuwa a Afirka ya ƙaru – WHO

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya yi wannan furucin ne a wajen wani bikin ƙaddamar da littafi a kansa, musamman ma yadda ya shahara wajen rubuta wa shugabannin Najeriya wasikar bankada ko tonun silili.

 

Advertisement

Ya ce tasirin kasar na fada a ji da kuma dadadden kallon da ake mata na babbar Yaya, kuma rumfa sha shirgi na ci gaba da raguwa musamman ma a kan kasashen nahiyar Afirka, sakamakon gazawa ko rashin tabuka abin kirki wajen jagorantar kannen nata.

 

Advertisement

Cif Obasanjon ya buga misali da wata gazawa da ya ce Najeriya ta yi wajen daidaita tsakanin shugabanni da ƴan tawaye a kasar Chadi – lamarin da sai da ƙasar Qatar ta dako gari daga nahiyar Asiya ta je ta shiga tsakani.

 

Advertisement

Tuni dai wasu masana huldar jakadanci suka fara tofa nasu albarkacin bakin a kan wannan maganar.

 

Advertisement

Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya ne, wanda ya ce duk da cewa Cif Obasanjo kan ji babu wanda ya yi komai in ba shi ba…a wannan ɓigiren ya fadi gaskiya.

 

Advertisement

Sai dai da BBC ta tambayi Ambasada Sulaiman Dahiru ko da wani abu da Najeriyar za ta yi don mai da martabar tata ta jagora ga kasashen nahiyar Afirkan?

 

Advertisement

Sai yace “A shekarun baya, an yi zamanin da Najeriya ta yi tasiri a kan kasashen Afirka da wasu kasashen duniya, musamman irin rawar da ta taka wajen yaki da nuna launin fata a kasar Afirka ta kudu da wasu makwabtanta.

 

Advertisement

Akwai ma lokacin da kasa irin Amurka ba ta daukar wani mataki a kan Afirka sai ta nemi shawarar Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending