Sports
Qatar 2022: Faransa ta doke Ingila, za ta kara da Maroko
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Faransa ta kai zagayen semi fiyanal a gasar kofin duniya da ake yi a Qatar, bayan da ta doke Ingila 2-1.
Faransa ta fara ci kafin aje hutun rabin lokaci ta hannun dan wasan tsakiyarta Tchoumeni.
To amma jim kadan bayan dawowa hutun ne Harry Kane ya farke wa Ingila a bugun fenareti.
Sai a minti na 78 kuma Oliviar Giroud ya ci wa Faransa kwallo ta biyu da kai, kuma jim kadan bayan haka Ingila ta sake samun bugun fenareti bayan da Hernandez ya ture Mason Mount a da’ira ta 18.To amma a wannan karon kyaftin din na Ingila Harry Kane ya barar da bugun fenaretin.
A yanzu Faransa za ta hadu da Maroko a zagayen kusa da karshe ranar Laraba.
To amma kafin nan sai Argentina ta kara da Croatia ranar Talata.
Za a buga neman na uku da kuma wasan karshe a ranakun Asabar da Lahadi.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
