Connect with us

News

Kirsimeti: Masu sayar da kaji sun yi kukan rashin ciniki a Gombe

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Sa’o’i kadan da fara gudanar da bukukuwan Kirsimeti, masu sayar da kaji a Gombe na koka wa da rashin ciniki.

A wata tattaunawa daban-daban da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a yau Asabar a Gombe, masu sayar da kajin sun ce yanayin abin damuwa ne.

Wakilin NAN da ya ziyarci sashen kasuwar kaji na babbar kasuwar Gombe, ya gano kwastomomi kaɗan ne su ka zo sayen kaji, yayin da aka lura akasarin masu sayar da kaji suna zaune a gefen kejin kajin sun yi tagumi.

Advertisement

Shugaban kungiyar masu sayar da kaji na jihar Gombe, Kabiru Musa ya ce farashin kajin ya dan kara tashi kadan idan aka kwatanta da na bara, 2021.

Musa ya ce duk da cewa kwastomomi kadan ne ke fitowa don sayen kaji, ya jaddada cewa yawan kwastomomin ya ragu matuka idan aka kwatanta da na 2021.

Ya yi bayanin cewa a shekarar 2021, ana siyar da balagaggiyar kaza a kan Naira 4,000 zuwa Naira 5,000 amma yanzu ta kai Naira 6,000 zuwa Naira 7,000.

Kaji balagaggu a 2021 ana siyar da su tsakanin N3,000 zuwa N4,000 amma yanzu yana kan N4,000 zuwa N6,000 gwargwadon girmansu.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending