News
Najeriya Ta Fi Kyau Kafin Zuwan Buhari inji Bishop Kukah
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban faston majami’ar yankin Katolika na Sakkwato, Matthew Hassan-Kukah ya ce duk da irin manyan alkawura da dama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, a yanzu zai bar ‘yan Najeriya “a matsanancin talauci” fiye da lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu, 2015.
Fusataccen malamin addinin ya kara da cewa baya ko tantama lafiyar Buhari ta karu a tsawon shekaru bakwai da rabi da suka shude amma yaso a ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun mori tagomashi daga ingantacciyar lafiyar da Buhari ya samu ta hanya damar samun ingantacciyar kulawa ta lafiya.
NDLEA ta kama mutum 12 bisa zargin shigar da tabar wiwi Najeriya
Dattijon malamin mai da’awa ya fadi hakan ne a sakon Kirsimetinsa na shekarar 2022.
Bishop Kukah ya ce “Mai girma shugaban kasa, ina taya ka da iyalinka murnar Kirsimeti. Ina magana ne a madadi na da sauran ‘yan Najeriya idan nace, mun gode Ubangiji da ya baka ingantacciyar lafiya.
“Mun sani cewa a yanzu kafi lafiya fiye da yadda kake a da. Muna ganin hakan ne da takunka, nisan tafiyar da kake ci gaba da yi kasashen ketare. Ubangiji ya karo maka maka shekaru cikin koshin lafiya.
Sai dai, Ina fatan miliyoyin ‘yan kasa sun samu damar morar wani bangaren daga cikin lafiyarka ta hanyar samun cigaba wajen inganta asibitocin kasarmu.
Bishop ya ci gaba da cewa “Abun takaici shi ne, duk da irin tarin manyan alkawuran da ka yi, zaka bar mu cikin matsanancin talaucin da yafi na baya da kazo ka same mu a ciki, wannan rashawar da muka yi zaton za a kawo karshenta ta zama ruwan dare.
“A sakona na Kirsimetin shekarar da ta gabata, na nuna yadda tayi wa dokar kasa hawan ‘kawara ta hanyar ragewa wajen girmama da bin dokokin dokar tarayya. Dukkanmu shaidu ne.”
Har ila yau, yayi jinjina ga shugaban kasa bisa kokarin da yayi a bangaren kayan masarufi sannan yana kokarin kawo karshen magudi a bangaren zabe.
