Connect with us

News

Ni na ajiye aiki ba korata aka yi ba – Baba Impossible

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Tsohom Kwmishinan harkokin addinai na jihar Kano Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya ce shi ya ajiye mukaminsa ba korarsa aka yi ba.

 

Advertisement

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa Dr Muhammad Tahar ya ce tun a ranar 30 ga watan Disamba ya kai wa sakataren gwamnati takardarsa ta ajiye aiki, kuma aka karba aka buga sitamfi aka ba shi nasa kwafin.

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya Kori Baba Impossible

Cikin takardar dai (Baba Impossible) ya ce bai bayyana dalilinsa na barin aikin ba.

Advertisement

 

Sai dai wata sanarwa da Gwamantin Jihar ta fitar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ta ce, Gwamnan Jihar Kano Abdullhai Umar Ganduje ne ya sanar da korar kwamishinan harkokin addini daga mukaminsa.

Advertisement

 

Kuma tuni aka bayar da sunan Dr. Nazifi Bichi a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Advertisement

 

Sanarwar ta ce “an kori kwamishinan ne saboda halin rashin da’a da yake nuna wa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami.

Advertisement

 

“An same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa a matsayin sana’a ta kashin kansa, har ma ya kan rage kwanakin aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, banda ranakun Laraba da Juma’a.”

Advertisement

 

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending