News
An yi taho mu gama da masu zanga-zanga da ‘yan sanda a Bolivia
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masu zanga-zanga sun yi arangama da ƴan sanda a Santa Cruz, birni mafi girma a Bolivia sakamakon gangamin yini guda da aka yi jiya Juma’a kan tsare gwamnan yankin bisa zarginsa da aikata ta’addanci.
Ɗaruruwan masu gangami sun jefa duwatsu tare da ƙona tayoyi yayin da ƴan sandan kwantar da tarzoma suka harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa su.
Yan sandan Jihar Edo sun kashe ‘yan fashi 58, sun ceto mutum 68 a 2022
An kama gwamnan kuma fitaccen jagoran hamayya, Luis Fernando Camacho ranar Laraba saboda hannu a wani rikicin siyasa da ya tilasta wa Shugaba Evo Morales ficewa daga ƙasar a 2019.
Mista Camacho dai ya musanta aikata ba dai-dai ba inda ya bayyana kama shin a matsayin yin garkuwa da shi.
Advertisements
