News
Boka Ya Mutu Yana Lalata Da Matar Fasto
Wani fitaccen boka mai suna Fadayomi Kehinde da ake yi wa lakabi da (Ejiogbe) a garin Ikere-Ekiti a Jihar Ekiti ya mutu a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake lalata da matar wani Fasto a otel.
Ana zargin matar Faston tana dauke da wani tsafin Yarbawa da ake kira Magun (Tsawa) da mijinta ya yi ba tare da saninta ba.
Ya kamata Gwamnatin Tarayya Ta Gaggauta Janye Karin Kudin Wutar Lantarki – SERAP
Yarbawa sun camfa cewa Magun yana hallaka duk mutumin da ya yi lalata da matar aure nan take kamar yadda ya rutsa da Boka Ejiogbe.
Matar Faston da aka sakaya sunanta ta yi wa jami’an tsaro bayanin cewa jim kadan bayan bokan ya gama lalata da ita a cikin dakin sai ya fadi kasa yana shure-shure da neman ta taimaka masa ta gayyato masu kula da dakunan otel din domin ceton ransa.
Aminiya ta rawaito cewa A lokacin da aka kai bokan wani asibiti a garin na IkereEkiti, likitocin sun tabbatar da mutuwarsa tun kafin su fara yi masa aiki.
Mutuwar Boka Ejiogbe ta sa wasu fusatattun mabiyansa sun cocin da Faston kuma mijin matar yake shugabanci inda suka lalata wasu sassan ginin cocin.
Matar Faston tana tsare a hannun ’yan sanda suna yi mata tambayoyi tare da kare ta daga fadawa hannun fusatattun mabiya bokan.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
