News
Almundahanar N96bn: Wike Ya Sake Maka Dan-Amanar Daura Amaechi A Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin na zargin Amaechi da yin sama da fadi sa biliyan 96 lokacin da yake gwamnan jihar.
Gwamnatin Ribas ta shigar da sabuwar kara kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri, Dan Amanar Daura Rotimi Amaechi, kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96.
An maka Amaechi tare da Tonye Cole, dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar bisa zargin sayar da kadarorin jihar.
Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata
Zacchaeus Adangor, babban lauyan Gwamnatin Jihar Ribas, ya tabbatar da shigar da karar.
Nyesom Wike, gwamnan Ribas, ya kafa wani kwamitin mutum bakwai don bincikar Amaechi kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna.
Kwamitin ya kuma binciki batutuwan da suka shafi sayar da kadarorin da tsohon gwamnan ya yi.
Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a 2015 kan binciken, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa.
A ranar 27 ga Mayu, 2022, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kansa.
Sakamakon haka ne, Wike, ya umarci babban lauyan jihar da ya gurfanar da tsohon gwamnan tare da Tonye Cole da wasu mutum biyar da ake zargin na da hannu a badakalar.
Wike ya kuma umarci a shigar kan kamfanin Sahara Energy, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen satar kudaden.
