News
Cunkoson mutane ya fara yawa a bankuna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Al’umma da dama sun bazama zuwa bankuna domin mayar da tsofaffin kuɗaɗensu, duk da cewa har yanzu mutanen Najeriya da yawa ba su ma fara ganin sababbin kuɗaɗen ba.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa a jihar kano , an fara ganin dogwayen layukan jama’a a cikin rana, suna ƙoƙarin mayar da kuɗaɗen nasu don gudun asara.
Hatsarin mota yaritsa da Fadawan Shehun Borno uku sun ƙone ƙurmus
Wasu daga cikin waɗanda jaridar indaranka ɗin ta tattauna da su sun bayyana fushinsa game da yadda wannan lamari yake gudana tare da bayyana cewa da babban bankin ƙasa (CBN) zai ɗan gusa da lokacin da aka ƙayyade, to da hakan ya taimakawa jama’a.
Haka su ma dai ma’aikatan bankunan da dama sun rasa yadda za su yi da jama’a. Wasunsu suna da ƙoƙari don ganin sun karɓi kuɗaɗen, wasu kuma a wajensu,
