News
Damisa ta biyu ta tsere daga gidan kula da namun dawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata damisa ta tsere da safiyar Litinin daga wata gonar da ake ajiye da ita a Afrika ta Kudu, mako biyu bayan da wata damisar ta tsere.
Al’ummar Edenvale da ke lardin Gauteng sun ga wata damisa tana yawo a yankin, kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.
A farkon wannan watan wata damisa ta tsere daga wata gona a yankin Walkerville na lardin Gauteng inda ta kwashe kwanaki tana kai hare-hare har ta raunata wani mutum da wani kare da kuma wani alade kafin daga baya a harbe damisar.
Wata hukuma mai rajin kare dabbobi daga ketar da ake musu, NSPCA ta tabbatar da ganin damisar, ta kuma bukaci hukumomi su dauki matakan kama ta baya ga gargadin jama’a su killace dabbobinsu na gida.
Sai dai daga baya tashar yada labarai News24 ta sanar da an yi nasarar kama damisar, kuma an kai ta wani wurin da za a killace ta.
