Politics
Da dumi -dumi:Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da Laila Buhari a matsayin Yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a PDP
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun daukaka kara a ranar Alhamis,Ta sake jadda da Hajiya Laila Buhari a matsayin Yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a Jami’iyyar PDP.
Solacebase ta rawaito cewa kotun Ta sake ayyana Laila Buhari ne sabanin Danburan Nuhu.
Gini ya ruguje a Abuja, ana fargabar mutane da yawa sun makale
Hukuncin wanda Mai Shari’a Muhammad Lawal Garba ya jagoranta, ya ki amincewa da dau kaka karar da Danburam Nuhu ya yi yana kalubalantar Laila Buhari.
Mai Shari’a Garba dai ya yanke hukuncin ne a tare da mai Shari’a Kudirat Kekere Ekun, da mai Shari’a Ibrahim Jauro, da kuma mai Shari’a Emmanuel Agim wanda duka suma sun shaida yadda zaman kotun ya gudana. I’ll
Advertisements
