News
Yanzu-Yanzu: Jam’iyyu 13 Na Barazanar Janyewa Daga Zaben 2023 Saboda Sake Fasalin kudi
DAGA ABDULRASHEED MUHAMMAD RABIU
Jam’iyyu 13” daga cikin 18 na Najeriya sun yi barazanar ficewa daga zabukan da za a yi a kasar bab a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris, sakamakon sake fasalin tsarin Naira da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
A wani taron manema labarai da gamayyar shugabannin jam’iyyun siyasa suka yi a ranar Litinin, “jam’iyyu 13” sun yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sake fasalin takardun kudi na N200, N500 da N1,000.
Ana zargin Man City da karya dokar kashe kudi fiye da abin da ta samu
Jam’iyyun sun ce ba za su yi sha’awar shiga zaben ba idan aka kara wa’adin amfani da tsohon daga ranar 10 ga Fabrairun shekarar 2023 kamar yadda wasu gwamnonin jam’iyyar suka bukata.
Jam’iyyu 13 sun kuma caccaki gwamnatin jihar Kaduna da Kogi da kuma Zamfara da suka garzaya kotun koli domin samun umarnin kotu na tsawaita wa’adin tabbatar da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin guda uku.
Shugaban kungiyar Action Alliance na kasa, Kenneth Udeze, wanda ya yi wa manema labarai karin haske, kan batun ya ce, “Muna sanar da cewa akalla jam’iyyun siyasa 13 cikin 18 a Nijeriya ba za su yi sha’awar shiga zaben 2023 ba, kuma lallai za mu janye mu daga shuga zaben idan an dakatar da wannan manufofin kudin ko kuma an soke ko kuma idan an kara wa’adin da aka bada.
