Connect with us

News

Yunkurin gurfanar da AA Zaura a kotu ya sake gamuwa da cikas

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Yunkurin hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, na gurfanar da ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Kano AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura kan zarge-zargen tafka damfara ya sake fuskantar cikas a kotu.

 

Advertisement

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ɗage gurfanar da A.A Zaura don bai wa sabon lauyansa dama ya je ya shirya don tunkarar shari’ar.

Yanzu-Yanzu: Jam’iyyu 13 Na Barazanar Janyewa Daga Zaben 2023 Saboda Sake Fasalin kudi

EFCC na zargin sa ne da damfarar wani ɗan ƙasar Kuwait kuɗi fiye da dala miliyan daya, zargin da ya sha musantawa.

Advertisement

 

Duk da kasancewar EFCC ta sami nasarar kawo AA Zaura gaban kotun tarayyar amma kotun ta ɗage zaman shari’ar saboda sabon sauyansa Basil Hemba bai shirya ba, inda yace yana buƙatar nazarin yadda zai tunkari batun kasancewarsa sabo kan shari’ar.

Advertisement

 

Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ta nemi kotu ta ci gaba da sauraron shari’ar saboda ta ce sun shirya kuma sun kawo wanda ake zargin kotu, sai dai sabon lauyan AA Zaura ya ce bai shirya ba kasancewar jiya ya karɓi kunshin Shari’ar.

Advertisement

 

Wannan shi ne karo na shida da ake ƙoƙarin gurfanar da AA Zaura, amma har yanzu ba a kai ga karanto masa zarge-zargen da EFCC ke masa a gaban babbar kotun tarayyar ba.

Advertisement

 

Saboda a cewar Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ana ta gabatar da uzuri iri daban-daban.

Advertisement

 

Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya ɗage zaman kotun zuwa 1 ga watan Maris, don bai wa sabon lauyan damar nazartar ƙunshin Shari’ar.

Advertisement

 

Bayanai na cewa wata babbar kotun tarayya a 2020 ta sallami AA Zaura tare da wanke shi kan da duk wani zargi da EFCC ke masa, abin da yasa EFCCn sake gabatar da zargin zamba da ake yi masa tun da farko a kotu.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending