News
Sake fasalin Naira: buhari ya nemi afuwar Yan Nigeria
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan batun sake fasalin sauya wasu daga cikin takardun kudi a Nigeria
Yau INEC Za Ta Ci Gaba Da Karbar Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Abuja
A cewarsa, ba a bullo da sauya takardun kudi don haifar da wahala ba, amma anyi hakanne kawai domin habbaka tattalin arziki
A watan Oktoban 2022, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin kudin N200, N500, da N1,000.
Babban bankin ya kuma ce ranar 10 ga watan Fabrairu ne za a kayyade amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira wanda hakan ya haifar da karancin kudin.
A wani faifan bidiyo da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani, ya saka a shafin Twitter a ranar Alhamis, Buhari ya ce: “Ina ba ku hakuri kan wahalhalun da canjin Naira ya haifar.
“An yi hakan ne domin bunkasa tattalin arzikin kasa, ba don a jawo wa kowa wahala ba.
