Connect with us

News

Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli  

Published

on

 

 

Advertisement

Duk da umarnin kotun koli kan tsohon kudi, wani bincike yayi nuni da cewa masu sana’o’i da kuma direbobi a a sassan kasar nan na ci gaba da kin karbar tsohon kudin tare da bayyana cewa sai sun ji amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kan hukuncin kotun.

 

Advertisement

Tun da farko kotun kolin ta yi umarnin cewa a cigaba da karbar tsohon kudi har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, inda ta yi watsi da wa’adin babban bankin kasa CBN.

’Yan Bindiga Sun Kashe DPO A Zamfara

Sai dai, a sabon hukuncin da kotun kolin ta yanke ranar Juma’a, kotun kolin ta ce tsohon kudin zai cigaba da zama halattace har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, tare da yin watsi da sauya fasalin takardun kudin. Kotun kuma ta ce ba a bai wa mutane isasshen wa’adi ba idan akayi la’akari da sashe na 20 na kudin dokar CBN na 2007.

Advertisement

 

Bisa wannan dalili, babban bankin kasa zai tsawaita halaccin kudin zuwa 31 ga watan Disamba, 2023, bisa dalilin cewa kasashe da dama suna barin sabo da tsohon kudi su zagaya a tare akalla na shekara guda. Idan za a iya tunawa a Disambar 2022, babban bankin kasa CBN ya sanar da sauya fasalin N200, N500 da kuma 1,000 daga 10 ga watan Fabrairu 2023.

Advertisement

 

Dalilin haka, gwamnonin kasar 16 suka nuna rashin amincewa da dokar, tare da shigar da karar gwamnatin tarayya, su na rokon kotun da ta dakatar da dokar.

Advertisement

 

Kotun kolin ta yi hukunci bisa abin da gwamnonin suka bukata, tana mai dakatar da gwamnatin tarayya daga wa’adin 10 ga Fabrairu. Amma akwai rashin tabbacin ko kotun na da ikon yin hukuncin, kamar yadda ake ganin ko babban bankin kasa, ma’aikata mai zaman kanta, zai bi umarnin kotun tun da shi aka shigar kara ba.

Advertisement

 

Duk da cewa, hukuncin kotun na ranar Juma’a abu ne da aka dade ana jira don saukaka al’amura, sai dai, a wasu wuraren kasuwanci kamar Ajah, Orile, Alaba da ke Legas da wasu a Abuja har da ma Kano, sun ce ba za su karbi kudin ba har sai sun jira babban bankin kasa CBN ko gwamnatin tarayya sun fitar da sanarwar amincewa da hukuncin duk da bayanin da kotu ta yi na cewa ba za a iya fasa canja kudin ba biyo bayan ganawar sirri da gwamnan babban bankin kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending