Connect with us

News

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan masunta a Borno

Published

on

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Alla-wadai da kisan fararen hula akalla 37 a wani harin kwantan ɓauna a ƙauyen Mukdolo a karamar hukumar Ngala na jihar Borno.

Rahotanni sun ce gwamman mutane ne waɗanda akasari manoma da masunta aka harbe a harin da ake zargin mayaƙan ISWAP da kai wa.

Advertisement

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli kasar nan ta tabbatar da Sanata Rufai Sani Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya

Harin ya faru ne a garin Dikwa wanda ke kusa da garuruwan da ‘yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram ke da karfi.

Mutane da dama ne suka jikkata a harin yayin da wasu da yawa kuma suka ɓata. An kashe manoman ne a ranar Laraba lokacin da suka je daji neman itace.

Advertisement

Majiyoyin tsaro sun ce gwamman mayaƙan na ISWAP sun yi wa garin dirar miƙiya a kan babura, inda bayan isarsu suka fara harbi kan mai uwa da wabi. Mutum tara ne kuma suka samu damar tserewa.

A cikin wata sanarwar da ofishin kodinetan ba da agaji na MDD Mista Mathias Schmale ya fitar, ya mika ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.

Advertisement

Ya ce akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su masunta ne da manoma waɗanda ke neman samun abin da dogaro da rayuwarsu.

“Wannan harin abin tayar da hankali ne kuma hakan ya sake nuna barazana da halin rashin tsaro da ‘yan gudun hijira da sauran mutanen da ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-baya na shekara sama da 13 ay shafa ke ciki a yankin. Mutane sun tserewa ƙauyen Mukdolo kafin kawo wannan hari sanadiyyar ayyukan kungiyoyi masu ikirarin jihadi,” in ji sanarwar.

Advertisement

Mista Schmale ya yi kira ga hukumomin jihar da suka gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da nufin hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending