Connect with us

News

ajeriya na binciken jirgin Lufthansa kan zargin cin zarafi

Published

on

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ta fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin fasinjoji sama da 200 da suka nufi Najeriya a jiragen sama na Lufthansa na ƙasar Jamus.

Kafofin yaɗa labaran sun ce jirgin ya yi barazanar kiran ‘yan sanda a ranar Juma’ar da ta gabata bayan fasinjojin da jirgin ya ɗauka suka bukaci a samar musu da wurin zama bayan jinkirta tashinsu.

Advertisement

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli kasar nan ta tabbatar da Sanata Rufai Sani Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin da ya fito daga Frankfurt zuwa Legas, da aka tsara zai sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, amma sai da ya yada zangon a Cotonou a ƙasar Benin da Malabo na ƙasar Equatorial Guinea.

Kamfanin Lufthansa ya nemi afuwar jinkirin da jirgin ya samu a wata wasika da ya aike wa fasinjojinsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Advertisement

Fasinjojin sun yi zargin cewa ba a rufe filin jirgin sama na Legas ba, saɓanin iƙirarin da matukin jirgin na Lufthansa ya yi.

Sam Adurogboye, jami’in hulɗa da jama’a na NCAA, a ranar Alhamis ya ce hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin bayan samun koke-koke daga fasinjojin. BBC ta tuntubi kamfanin jirgin domin jin karin bayani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending