Connect with us

News

Kotu ta ɗaure waɗanda suka yi wa ƴan Birtaniya fyaɗe a Ghana

Published

on

Wata babbar Kotu a Ghana ta yanke wa wasu mutum uku ɗaurin shekara 73 a gidan yari saboda yi wa wasu yan mata guda huɗu ‘yan asalin Birtaniya fyaɗe.

An kuma samu mutanen uku da laifin yi wa yaran fashi, a lokacin da suke wata ziyara a Ghana.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan masunta a Borno

Mutanen da suka haɗa da ‘yan Najeriya biyu da wani ɗan Ghana sun amsa laifin zargin da aka yi musu wanda ciki har da mallakar bindiga ba bisa ka’aida ba.

Alkalin Babbar Kotun da ke Accra, ya yanke musu hukuncin daurin shekara 24 saboda laifin fashi da makami, da kuma shekara 24 saboda aikata fyaɗe, sai kuma ƙarin wasu shekaru 25 a kurkuku saboda mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

Mutanen za su yi zaman hukucin ne a lokaci ɗaya, wanda ke nufin zaman shekara 25.

Shari’ar dai an gudanar da ita ne a cikin sirri domin gudun bayyana yaran da aka yi wa fyaɗen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending