Connect with us

News

Tsohuwa Ta Kona Danta Da Iyalansa

Published

on

 

Ana zargin wata tsohuwa mai shekaru 75 ta cinna wa danta, jikokinta biyu da kuma surukarta wuta a Jihar Ondo.

 

Ana zargin dattijuwar ta yi ajalin dan nata da iyalansa ne bayan ta watsa musu fetur sannan ta cinna musu wuta a cikin gidansu, lamarin da ya haddasa mummunar gobara.

Napoli Na Shirin Lashe Serie A Karon Farko Cikin Shekara 33

 

Rahotanni na nuni da cewa abin ya faru ne a wani kauye da mai suna Aponmu da ke wajen garin Akure, babban birnin jihar.

Advertisement

 

Majiyarmu ta shaida mana a ranar Talata cewa an kai magidancin da iyalan nasa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo, inda likitoci suka tabbatar cewa shi da matarsa da daya daga cikin yaran sun rasu.

 

 

“Babban dan ne kadai ya rayu, shi ma din a yanzu haka yana cikin mawuyacin hali,” in ji shaidar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending