News
Za A Fuskanci Tsananin Zafin Rana A Wasu Jihohin Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a faɗin wasu jihohin ƙasar ƙasar.
INEC ta sanya ranar bai wa zaɓaɓɓun gwamnoni shaidar cin zaɓe
Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun ƙunshi Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.
Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.
A cikin wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce hukumar ta lura da cewa yanayin zafin rana zai kai maki 40 a ma’aunin celcius a cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.
NiMet ta yi gargaɗin cewa jihohi kamar a Bauchi da Gombe da kuma Adamawa na cikin haɗarin rashin jin daɗi musamman a ɓangaren lafiyarsu.
Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.
Ta kuma shawarci masu azumi da kar su riƙa fita cikin ranar, sannan kuma su riƙa shan wadataccen ruwa a lokatan shan ruwa da sahur.
Hukumar ta Nimet ta kuma tabbatar wa mutane cewa za ta ci gaba da bibiyar yanayi don sanar wa al’umma halin da ake ciki.
