Connect with us

News

Matana Da ’Ya’yana Ba Za Su Shiga Gwamnatina Ba — Abba Gida-Gida

Published

on

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, ya yi alkawarin cewar matansa da ’ya’yansa ba za su samu wani mukamin da zai ba su damar shiga sharafin gwamnatinsa ba.

Yusuf, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar takardar shaidar lashe zaben Gwamna a ofishin INEC da ke jihar, ya bayyana hakan ne kan yadda ake zargin iyalan gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka yi tasiri wajen tafiyar da gwamnatin jihar.

Advertisement

Za A Fuskanci Tsananin Zafin Rana A Wasu Jihohin Najeriya

Zababben gwamnan ya ce ba zai bai wa iyalansa damar shiga gwamnatinsa ba saboda ba tare aka rantsar da su ba domin yi ea al’ummar Jihar Kano aiki ba.

“Matana ba za su kasance a gwamnati ba. ’Ya’yana ba za su kasance a cikin gwamnati ba. Kuma ina tabbatar muku da cewa mataimakina ma hakan ce za ta kasance,” a cewarsa.

Advertisement

Abba ya bukaci dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da sauran wadanda suka yi takara da su zo a yi tafiya tare don ciyar da Jihar Kano gaba.

“Mun samu labarin Gawuna ya sanar da kafafen watsa labarai kafin bayyana sakamakon zabe cewa idan bai yi nasara ba, zai karbi abin da Allah Ya kaddara. Don haka muna kira a gare shi da ya fito ya ja hankalin mutanensa su yarda da cewar wannan yin Allah ne,” in ji shi.

Advertisement

Ya ja hankalinsu da su yi koyi da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya fadi zabe a 2003 amma ya taya wanda ya lashe zaben murna.

Da yake magana game da gudunmawar jami’an tsaro a lokacin zaben gwamna a jihar, Abba ya gargadi jami’an tsaron da suka hada kai da jam’iyya mai mulki da su guji aikata hakan a gaba, inda ya bukace da su fifita hidimtawa ‘yan Najeriya ba tare da nuna wariya game da jam’iyya, Addini ko kuma kabilanci ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending