Connect with us

News

Kotu ta yankewa Zakara hukuncin kisa a KANO

Published

on

 

Wata kotun Majasteri da ke da zama a gidan Murtala a birnin Kano, ta umarci wani mutum mai suna Isyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en da ya yanka Zakaransa.

Advertisement

Tun farko dai wani maƙwafcinsa ne mai suna Malam Yusuf Muhammad Ja’en, ya shigar da ƙara gaban Kotun, yana mai cewa, Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.

Amma koda aka karantowa wanda ake ƙara, sai ya ce, gaskiya ne Zakaran nasa na yawan yin Cara, kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

Advertisement

Mai shari’a Halima Wali ta amince inda ta umarci mutumin da ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a ranar Juma’a mai zuwa wato ranar “Good Friday” ɗin.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending