Connect with us

News

‘Yan Siyasa Ne Suke Kokarin Raba Kan Al’ummar Najeriya

Published

on

 

Tsohon Ministan harkokin matasa a Najeriya Barrister Solomon Dalong ya bayyana mahimmancin dake akwai ga al’ummar Najeriya mabiya addinin Kirista da Musulunci su zauna lafiya da juna.

Advertisement

Tsohon ministan yayi wannan bayanin ne a wurin wani taron cin abincin da shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Bauchi ya saba shiryawa kowace shekara a jihar Kaduna.

 

Advertisement

An Gano Sabon Irin Shinkafa Mai Jure Ambaliyar Ruwa

Ya kuma jaddada cewa, kasancewar Allah ya kasa al’ummar Najeriya masu addinai daban-daban kuma karkashi kabilu mabanbanta alkahiri ne da ya kamata mu ribace shi ta hanyar hada kawunan mu.

Yayi bayani a game da babban zaben kasar da aka gudanar tsakanin watan biyu da watan jiya inda ya ce duk da cewa an kammala zabe, zaben ya bar baya da kura kuma kamata yayi mutane su kiyaye duk wani abinda zai raba kansu.

Advertisement

Shararren malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi a cikin jawabinsa a wurin taron, yace duk dan siyasar da zai hada kan al’umma ba tare da nuna banbanci ba, shi ya dace da shugabancin Najeriya, kana ya nuna cewar Allah ya hallice mu domin mu fahimci juna sannan mu taimakawa juna ba domin raba kawunan mu ba kuma ya ce duk wanda yake ji ba ayi mishi adalci ba a zaben da aka gudanar, kotu ce sahihin hanyar da doka ta tanadar domin neman hakkin mutum.

Pastor Yohana Buru wanda shi ma ya hallarci taron cin abincin da aka yi a gidan shahararren mallamin, ya ce kamata yayi mutane su yiwa Allah godiya da ya yadda Allah ya hallice mu kuma su fahimci masu neman janyo rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending