Connect with us

News

Majalisar Najeriya ta gayyaci ministoci kan bacewar gangunan danyen mai

Published

on

 

Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin batar gangar danyen mai miliyan 48 a kasar ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari’a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar domin bayar da bahasi a game da wannan badakalar.

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami’an gwamnatin kasar da karkatarwa zuwa China.

Advertisement

An yi gwanjon takalmin Michael Jordan kan Dala miliyan 2.2

Da yake magana kan rashin girmama gayyatar da kwamitin ta ya yi wa Ministocin Kudi da na Shari’a da wasu jami’an hukumomin gwamnatin kasar, Shugaban Kwamitin Binciken Hon. Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi Zainab Ahmed da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.

 

Advertisement

Ya ce a daya bangaren kuma, ana zargin Ministan Shari’a na kasar da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa, kwamitin na da bayanan sirri na wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba su bin ka’idar amfani da tsarin asusun ajiyar kudi na bai-daya.

 

Advertisement

Sai dai bai bayyana ranar da jami’an gwamnatin za su bayyana a gaban

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending