Connect with us

News

Majalisar Dattawa Ta Kafa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

Published

on

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 45 da za su yi aikin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Advertisement

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da kafa kwamitin a ranar Laraba, yana mai cewa za a kaddamar mambobin a ranar Talatar makon gobe kuma nan take za su fara aikin.

Ana shirin mayar da wasu ofisoshin Hukumar NUPRC zuwa Legas

Akpabio bayyana cewa kundin tsarin mulki na 1999 yana bukatar sake dubawa, saboda a cikinsa akwai batutuwa da dama da ya kamata a gyara su.

Advertisement

Ya ce kwamitin yana da wakilcin sanata daya daga kowace jiha da kuma Abuja, sai kuma wakili daya daga kowace shiyyar siyasar kasar nan.

Sanata Akpabio ya bukaci a gabatar da duk shawarwari da bangororin kundin tsarin mulkin kasar da ake bukatar su yi wa kwaskwarima wa kwamitin.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaban majalisar ya kuma umarci kwamitin ya gayyaci shugaban majalisar dokokin kowace jiha domin tattaunawa da ba da gudummawarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending