Connect with us

News

An Maka Wata Mata A Kotu Bisa Karya Ƙafar Ma’aikacin NEPA Yayin da yaki Ƙoƙarin Yanke Mata Wuta

Published

on

 

Wata mata mai shekaru 34 mai suna Nosimot Alalade, a ranar Juma’a, ta gurfana a gaban wata kotun Majistare da ke Abeokuta, a Isabo bisa laifin cin zarafin ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan, IBEDC, a lokacin da ya ke gudanar da aikin sa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa  NAN ya ruwaito cewa wacce ake zargin na zaune ne a lamba 5, titin Amadiya, unguwar Olomore a Abeokuta.

 

Kylian Mbappe ya kafa sabon tarihi a  PSG

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya kuma ruwaito cewa waccw ake karar na fuskantar tuhume-tuhume guda uku na cin zarafi, tada zaune-tsaye da kuma yin abin da zai jefa rayuwar mai korafin cikin hadari.

Mai gabatar da kara, Sifeto Olaide Rawlings, ya shaidawa kotun cewa wacce ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Afrilu da misalin karfe 1:00 na rana a unguwar Olomore dake Abeokuta.

Advertisement

Ms Rawlings ta ce wacce ake tuhumar ta ci zarafin wani Silas Olaleye ta hanyar turo shi daga kan tsani yayin da ya ke gudanar da aikinsa na halal, wanda hakan ya jawo masa karaya a kafarsa ta dama.

A cewarta, laifukan sun saɓa wa sashe na 338, 343, 355 da 249 na kundin laifuffuka na jihar Ogun, 2006.

Sai dai wacce ake tuhumar musanta laifin da ake tuhumar ta da shi.

Alkalin kotun, M.O. Osinbajo, ta bayar da belin wacce ake kara a kan kudi N100,000, tare da mutum daya da zai tsaya mata.

Bayan haka, ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga Afrilu domin ci gaba da shari’ar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending