Connect with us

News

An Kashe ’Yan Boko Haram 35, Wasu 135 Sun Mika Wuya A Borno

Published

on

 

 

 

Yan ta’addan Boko Haram sun sheka lahira, wasu akalla 135 tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

 

Mika wuyan ’yan ta’addan ya biyo bayan karin farmakin da sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) suke kai musu ne a Dajin Sambisa.

Advertisement

 

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 40 A Kebbi Da Zamfara

“An kashe kusan ’yan ta’adda 35 a aikin hadin gwiwa a Kananar Hukumar Bama,” in ji wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a Yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama.

 

“Akwai karin ’yan ta’adda 113 daga garuruwan Balangaje da Bula-Waziri da Bula – Kurma da Sabil – Huda wadanda suka mika wuya ga sojoji a Yamteke,” in ji shi.

 

 

Advertisement

Ya bayyana a Maiduguri cewa ’yan ta’addan sun ajiye makamansu ne mako guda bayan sojoji da makan sa kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) sun tsananat kai farmaki a maboyarsu.

 

Zagazola ya ce wasu karin ’yan ta’addan tare da iyalansu da suka hada da kananan yara 13 da mata daga kauyukan Nguru Soye da Kelani sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 202 da ke Bama.

 

Hakazalika, namiji daya da mata biyar da yara shida daga kauyukan Kauri da Siraja da Lene Hassana sun mika wuya ga sojoji a Mahadar Banki da ke kan hanyar Bama-Gwoza.

 

Advertisement

 

Ya ce duk tubabbun ’yan ta’addan na Boko Haram an mika su ga hukuma domin kula da su da mika su ga iyalensu.

 

 

Babban Kwamandan Runduna ta 7 ta Sojin Najeriya, Manjo-Janar AE Abubakar, ya jinjina wa sojojin sannan ya bukaci su fatattaki ’yan ta’addan domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending