News
Kotu a Birtaniya za ta yanke wa Ekweremadu da matarsa hukunci a yau
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci.
Wannan ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam a watan Maris.
Za Mu Ɓullo Da Matakan Da Za Su Hana Alƙalai Kwaɗayin Cin Hanci – Tinubu
Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.
Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.
An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London.
Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
