News
Kano: Gwamnati Da NDLEA Sun Shirya Kawo Karshen Shaye Shaye A Tsakanin Matasa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya karkade ƙafarsa, a jiya Litinin domin yaki da matsalar shaye shaye a tsakanin al’ummar jihar, jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan Kano.
Gwamnan tare da shugaban hukumar NDLEA Abubakar Idris Ahmad a jiya sun kai ziyara gidan gyaran hali na Ƙiru, wanda ake kula da matasa masu fama da matsalar shaye shaye, wanda hakan na daya daga cikin manya-manyan matakai na magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
Saudiyya da Amurka sun yi maraba da tsawaita yarjejeniyar Sudan
Ziyarar da sabon gwamnan ya kai tare da kwamandan hukumar na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya nuna shirin gwamnatin na yin hadin gwiwa da hukumar domin dakile matsalar shan miyagun kwayoyi a jihar.
Kawar da barazanar miyagun ƙwayoyi ya zama babban abin damuwa a duniya.
Sanarwa daga ASN II Sadiq Muhammad Maigatari, mai magana da yawun hukumar NDLEA, ya ce gwamnan da Kwamandan sun yi tattaunawa mai ma’ana kan yadda za a dakile matsalar yadda ya kamata.
Maigatari ya bayyana cewa hukumar NDLEA reshen jihar Kano na godiya da goyon bayan da gwamnan ya bayar wajen wannan yaki da shan miyagun kwayoyi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
