Connect with us

News

Adadin wadanda suka mutu a rikicin Senegal ya kai 15

Published

on

DAGA  KABIRU BASIRU FULATAN

 

Bayan yanke wa dan jagoran adawar Ousmane Sonko hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, bisa samunsa da laifin lalata da wata budurwa bayan an wanke shi kan zargin aikata fyade, a ranar Alhamis rikici ya barke da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6.

A ranar Juma’a kakakin gwamnatin kasar Maham Ka ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewar an samu karin mutuwar mutane 4 a babban birnin kasar Dakar da kewayen sa, sannan kuma wasu mutum biyu suka mutu a Zinguinchor.

Real Madrid ta soke kwantiragin Eden Hazard daga kungiyar

An wasushe kayayyaki a gine-ginen gwamnati da na ‘yan kasuwa da bankuna, bayan fito na fito da aka yi tsakanin jam’ian tsaro da matasan da ke zanga-zanga.

Ma’aikatar kulada harkokin cikin gida ta kasar ba ta bada rahoton samun wani sabon riciki da sanyin safiyar yau Asabar ba, yayin da har yanzu akwai sojoji jibge domin tallafawa ‘yan sanda.

Advertisement

Sonko da aka gudanar da shari’ar ba a gaban sa ba, har yanzu ba a kai shi gidan yari ba domin fara zaman wa’adin da aka yanke masa, duk da cewa ana ganin  zai iya haifar da wani tashin hankali.

Alamu na nuna cewar zai ci gaba da zama a gidansa da ke Dakar, inda jami’an tsaro suka tare shi tun karshen mako duk da cewa ya yi zargin cewa tsare da shin da jami’an tsaro ke yi ya sabawa ka’ida ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending