Connect with us

News

Tinubu Ya Rantsar Da Sabon Sakataren Gwamnati

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Sanata George Akume a masayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Tinubu ya rantsar da Akume ne a Fadar Shugaban Kasa a wani kwarya-kwaryan biki da ka shira, wanda manan mutane, ciki har da tsoffin gwamnoni da masu ci suka halarta.

Advertisement

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu ta nada mashawarta na musamman guda 20

An rantsar da Akume ne washegarin da Majalisa ta sahale wa shugaban kasa nada mutum 20 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Mahalarta sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Shugaban Malisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan;  Gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, sai kuma matar Akume, Regina.

Advertisement

Akume mai shekaru 69, ya zama Gwamnan Binuwai a lokacin yana da shekaru 45 — daga 1999 zuwa 2007.

Bayan saukarsa daga kujerar gwamna ne ya zama dan Majalisar Dattawa yana da shekaru 53 — daga 2007 zuwa 2019.

Advertisement

Yana da shekaru 65, a 2019 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi Ministan Ayyuka na Musamman, kafin yanzu Shugaba Tinubu ya nada shi Sakaaren Gwamnai a shekaru 69.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending