Connect with us

News

Tinubu ya janye rushe Hukumomin Gudanarwar NAFDAC da NDLEA

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Shugaba kasa Bola Tinubu ya janye rushe Hukumomin Gudanarwar Hukumar Daƙile Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi, wato NDLEA da kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci ta Ƙasa, wato NAFDAC.

Advertisement

Cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar, ta ce Hukumomin biyu ba su cikin waɗanda aka rusa.

Jihar kano zata kara rike kanbunta ta uwa a Arewa Idan aka habbaka harkokin Tarihi da Al’ada -bashir Hayatu jantule

Haka kuma Tinubu ya maida Hukumar NEMA da NAHCON ƙarƙashin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Advertisement

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannun maida Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA) da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) a ƙarƙashin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Ya maida su ne kamar yadda dokar Najeriya ta ce a can za su kasance tun farkon kafa su.

Advertisement

Daraktan Yaɗa Labaran Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Olusola Abiola ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Talata.

Dama kuma a cikin wata sanarwar Tinubu ya ce Hukumomin biyu ba su cikin waɗanda aka rushe.

Advertisement

Wasu Hukumomin Gudanarwar da Tinubu ya rusa sun haɗa da NUC, JAMB, NECO, TETFund, UBEC da wasu birjik.

Hukumomin Gudanarwar da Tinubu ya rusa sun haɗa da na jami’o’i, Kwalejojin Fasaha, JAMB, NUC da dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar ilmi.

Advertisement

Akwai NBAIS, NERDC, NMEC, NECO, LRCN, NBTE, NCCE, UBEC, CPN, TETFund, NABTEB, NTI, NINLAN, TRCN da sauran su.

Akwai kuma wasu Hukumomi 14 Waɗanda Tinubu bai rusa da guduma.

Advertisement

Akwai Hukumomi 14 waɗanda Tinubu bai rusa da guduma ba.

1. Hukumar Gudanarwar Lafafta Ma’aikata (CCB), wato Code of Conduct Bureau.

Advertisement

2. Majalisar Gudanarwa.

3. Hukumar Federal Character Commission.

Advertisement

4. Hukumar Ma’aikata ta Tarayya.

5. Hukumar Kula da Alkalai ta Ƙasa.

Advertisement

6. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.

7. Majalisar Tsaro ta Ƙasa.

Advertisement

8. Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa.

9. Majalisar Shari’a ta Ƙasa.

Advertisement

10. Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa.

11. Majalisar Harkokin Tsaro ta Ƙasa.

Advertisement

12. Hukumar Aikin ‘Yan Sanda ta Ƙasa.

13. Hukumar Ɗaukar ‘Yan Sanda ta Ƙasa.

Advertisement

14. Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga Ga Sassan Gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending