News
Cire Tallafi: Dole ‘Yan Siyasar Najeriya Su Sadaukar Domin Talakawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (TUC), Festus Osifo ya ce jami’an gwamnati ba su nuna ragi ba saboda har yanzu suna tafiya da ayarin motocin da ba su da iyaka, duk da illar cire tallafin man fetur ga talakawa.
Kwamared Osifo ya ce lokaci ya yi da ‘yan siyasa da masu fada aji za su kara sadaukarwar da kan su don amfanar da talakawan kasar nan.
“Misali, ayarin motocin. Ka ga gwamnoni har yanzu suna ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba. Ka ga sabbin ‘yan majalisa, ka ga ayarin motocinsu, ba su da iyaka,” in ji Osifo a gidan talabijin na Channels cikin shirin Siyasa a yau na ranar Laraba.
Osifo ya kuma yi tir da yadda ake kashe kudaden gudanar da mulki yayin da ya ja hankali kan raguwar kashe kudaden da ake kashewa.
“Yau har yanzu muna shigo da motoci iri-iri daga sassan duniya daban-daban duk da akwai wasu motocin da ake kera su a Najeriya.
“Me ya sa ba za ku iya samar da manufofin da za su karfafa masana’antu da kuma rage tsadar harkokin mulki ba?” Ya tambaya.
Osifo ya ce kungiyar kwadago ta gabatar da Naira 200,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi daga Naira 30,000 saboda ta yi hasashen cewa gwamnati ta karya darajar naira ta kuma baiwa ‘yan kasuwa damar tantance canjin kudin kasar.
Ya kara da cewa darajar Naira 30,000 shekaru biyar da suka gabata lokacin da aka sake duba mafi karancin albashi ya zuwa yanzu ya ragu tare da hauhawar farashin kayayyaki, farashin abinci da farashin sufuri da dai sauransu.
A cewarsa, kayan da aka ba wa jama’a ne kawai suke tafiya, ya bayyana mutane a matsayin manufa mafi sauki.
